KASATA NIGERIA: ƘASA MAI ALBARKA, AMMA...?
KASATA NIGERIA: ƘASA MAI ALBARKA, AMMA...?
Gabatarwa
Nigeria — ƙasa ce da take da albarkatu fiye da misali. Mai arzikin ma'adinai, ƙwararrun mutane, da matasa masu fasaha. Amma duk da wannan ni'ima, me yasa har yanzu muna cikin talauci, rashin tsaro, da rashin ci gaba? Shin matsalar shugabanci ce kawai? Ko kuwa akwai abin da 'yan kasa ke yi da bai daidai ba?
Ƙashin Bayani
Abin Da Dan Kasa Ke Yi Daidai:
1. Aiki Tuƙuru: Akwai matasa da dama da suke ƙoƙarin dogaro da kansu ta hanyar kasuwanci, sana’o’i, da ilimi.
2. Bin Doka: Duk da wahala, wasu har yanzu suna kokarin bin doka da oda.
3. Ƙaunar Ƙasa:Jama'a da dama na fatan Najeriya ta gyaru, kuma suna addu’a akai.
Amma Kuma...
1.Cin Hanci da Rashin Gaskiya: Yawancin mutane sukan nemi “hanya mafi sauƙi” ko da haramun ce.
2. Zubar Da Shara, Karya Doka: Mun saba da jefa shara a titi, kai da sauri fiye da ƙa’ida, ko amfani da wutar lantarki ba tare da biya ba.
3.Rashin Ƙaunar Juna: Muna yawan ƙin juna bisa bambance-bambance kamar addini da ƙabila.
Shugabanni Fa?
zan ciga a'wannan shafinawa mai albarka
Wannan rubutu na musamman daga: Abdulrahman Gambo Adam*
– Shafin da ke bayyana zuciyar al’umma.*

Comments
Post a Comment