Kalli bidiyon yadda ‘yan bindiga suka kone wani kauye a jihar Kebbi



Bayan Kashe Al'umma Da 'Yan Bindiga Suka Yi A Yankin Shanga Dake Jihar Kebbi, Sun Sake Dawo Sun Bankawa Wani Kauye Wuta

Bayan cikin jimami da radadin zafin rashin da da al'umma ke ciki na rashin rayuwar 'yan uwansu da 'yan bindiga suka kashe tare da garkuwa dawani, sun kara garzayowa wani kauye mai suna Tungar Zarumai suka bankawa garin wuta a jiya Asabar.

Dukiyar al'umma da kuma abincinsu duk sun salwanta, yayinda al'ummar kauyen kowa ya tsere domin tsira da rayuwarsu.

Har yanzu dai cikin zancen al'umma wannan yankin suna cikin fargaba a wannan karamar hukumar mulki ta Shanga. Wanda ake duban cewa matukar ba jami'an tsaro suka kawo dauki ba to tabbas  zasu Kara aikata wani mummunar ta'adin.

Comments

Popular posts from this blog

Petrol costs N1,826 in Togo, Dangote denies DAPPMAN’s petrol pricing claims

Good day. I'd like to talk about an important topic titled: ‘Nigeria’s Technology Industry: Opportunities in Technology, Media, and Telecommunications.

KASATA NIGERIA: ƘASA MAI ALBARKA, AMMA...?