Da Dumi Duminsa Kotun ɗaukaka ƙara ta kammala sauraron shari'ar zaɓen gwamnan Kano


Da Dumi Duminsa Kotun ɗaukaka ƙara ta kammala sauraron shari'ar zaɓen gwamnan Kano

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, ta kammala sauraron ƙarar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya ɗaukaka, kan hukuncin kotun ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar.

Yana dai ƙalubalantar hukuncin watan Satumba, wanda ya ce ɗan takarar jam'iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara, bayan kotun ta rage ƙuri'un Abba Kabir, sama da 160,000.

Bayan sauraron lauyoyin duka ɓangarorin, sai kotun ta ce ta ajiye hukunci, wanda ake sa ran za ta sanar kan wannan shari'a a ƙasa da mako biyu.

Babban lauyan gwamnan Kano, Wole Olanipekun ya roƙi kotun ta ba da damar sauraron ƙarar da suka ɗaukaka, sannan ta jingine hukuncin ƙaramar kotu gaba ɗayansa.

Ya yi iƙirarin cewa ƙaramar kotun ta ƙirƙiro wani sabon abu, wanda ya saɓa wa duk hukunce-hukuncen da kotun ɗaukaka ƙara, da Kotun Kolin ƙasar suka taɓa yankewa a baya.

Ya kuma ce hukuncin ƙaramar kotun kuskure ne, saboda wannan ne karon farko da wata jam'iyya a Najeriya, ta shigar da ƙara ba tare da ta sanya ɗan takararta a ƙorafin da ta yi ba, kuma duk da haka aka ayyana ɗan takarar a matsayin wanda ya yi nasara.

Sai dai babban lauyan jam'iyyar APC Akin Olujimi, ya ƙalubalanci matakin inda ya ce Kotunan Daukaka Kara sun yanke ƙarara cewa, rashin sa hannu a kan ƙuri'un da aka kaɗa, daidai yake da tafka maguɗin zaɓe.

Ya ce ƙa'idojin INEC sun zartar da abin da baturen zaɓe zai yi a rumfar kaɗa ƙuri'a, ciki har da tabbatar da sa hannu da kwanan wata a bayan kowacce ƙuri'a.

Ya ce a duk inda aka samu gazawar baturen zaɓe wajen yin abin da ya dace, hakan na iya zama an saɓa wa kundin dokar zaɓe.

Game da ɗan takarar APC wanda ba a sanya shi cikin ɓangarorin da ke cikin shari'ar a ƙaramar kotu ba, Mai shari'a Akin Olujimi ya ce tabbatacciyar doka ce cewa jam'iyya ake zaɓa a duk wani zaɓe da aka yi, kuma duk wani hukunci da ya shafi jam'iyyar siyasa, to ba shakka zai shafi duk 'ya'yanta.

A ɓangaren da APC ta ɗaukaka ƙara, jagoran lauyoyin APC, Akin Olujimi ya nemi kotun ta tabbatar da hukuncin cewa gwamnan Kano, ba ɗan NNPP ba ne, a lokacin da jam'iyyar ta tsayar da shi takara.

Sai dai, babban lauyan INEC A.B Mahmoud ya nemi kotun ta kori ƙarar da APC ta ɗaukaka, saboda rashin makama

A ranar 20 ga watan Satumba ne, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen Kano, mai alƙalai guda uku a ƙarƙashin Mai shari'a Oluyemi Akintan Osadebay, ta rushe nasarar Abba Kabir, bayan ta rage ƙuri'a 165,663 a cikin abin da ya samu.

Alƙalan kotun waɗanda suka karanta hukuncin da suka yanke ta manhajar Zoom, sun ce sun amince da hujjojin lauyoyin jam'iyyar APC.

Inda suka soke nasarar ɗan takarar NNPP, bayan sun ƙara da cewa ƙuri'u sama da 160,000 da ya samu "ba su da sa hannu ko hatimi ko kuma kwanan wata daga INEC".

Kuri'un Abba Kabir dai sun koma 853,939 daga 1,019,602, da hukumar zaɓe ta ce ya samu a watan Maris, tun da farko.

Lamarin dai ya sanya shi garzaya wa kotun ɗaukaka ƙara, inda ya buƙaci ta soke hukuncin ƙaramar kotu na watan Satumba.

Rahotanni sun ce su ma jam'iyyun APC da INEC da kuma NNPP, duk sun shigar da ƙorafe-ƙorafensu a gaban kotu dangane da hukuncin watan Satumba.







Daga BBC Hausa

Comments

Popular posts from this blog

Petrol costs N1,826 in Togo, Dangote denies DAPPMAN’s petrol pricing claims

Good day. I'd like to talk about an important topic titled: ‘Nigeria’s Technology Industry: Opportunities in Technology, Media, and Telecommunications.

KASATA NIGERIA: ƘASA MAI ALBARKA, AMMA...?