SUBHANALLAH, Yanzu-Yanzu Bom ya fashe a unguwar Shanono da ke jihar Kaduna
Rahotannin da ke shigo mana yanzu sun nuna cewa yanzu haka wani Bom ya fashe a unguwar Shanono da ke Karamar hukukar Rigasa ta jihar Kaduna. Wannan ya faru ne biyo bayan ta'addacin da aka yi a tashar jirgin kasa da ke Kaduna, da Kuma kashe matafiya da ake ta yi a hanyar Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja. Zuwa yanzu dai ba a tantance adadin mutanen da Suka rasa rai ba, da Kuma wadanda Suka ji raunuka. Cikakken rahoto na nan tafe.