Posts

Showing posts from February, 2022

An Kai Amarya Aisha Tsamiya Gidan Mijinta A Sabuwar Mota Fil A Leda

Image
 An kai Jarumar Fina-Finan Hausa na Kannywood, Aisha Tsamiya gidan Mijita, a cikin wata galleliya mota sabuwa fil. Wannan ya sanya cece-kuce a shafukan sadarwa na zamani, musamman Facebook Idan ba a manta ba a ranar Juma'a ne aka dauren Aisha Tsamiya, da Mijinta, wanda da ana hasashen an daga, Amma daga bisani aka gudanar da shi a Jihar Kano.

Tirkashi, za a fara binciken dalilin mutuwar shugaban kasar Libya Gaddafi

Image
Cikin Fushi Da Bacin Rai, Shugaban Rasha Vladimir Putin Ya Nemi Kungiyar Kasashen Turai (NATO) Da Su Fada Masa Dalilin Kisan shugaban Kasar Libya Ghaddafi  A cikin wani faifan Bidiyo na shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa kungiyar NATO kungiya ce ta kasashen Amurka, Ingila, da Faransa da kawayen su wadanda su ke yaki ta hanyar zalunci da danne kasashen da ba su kai karfin su ba. "Miye dalilin ku na kashe shugaban kasar Libya Muhammadu Al-Ghaddafi?" "Na sani cewa kun kashe shi ne saboda ya ki bin ku ne, saboda ya ki mara muku baya wajen ganin kun shigo kasar sa kun cutawa al'ummar sa". "Kun kashe shi, kun lalata kasar sa, kun kwashe dukiyar kasar sa saboda zalunci". "Wannan shine irin zaluncin da kungiyar NATO kuke aikatawa kasashen duniya musamman na Afriaca".  "Ghaddafi shugaba ne mai son kasar sa da cigaban ta, amman kun kashe shi akan zalunci kun kwashe dukiyar kasar"Inji shi Daga: S-bin Abdallah Sokoto

Wani Matashi Ya Auri Mata Biyu A Lokaci Guda A Jihar Adamawa

Image
 Rahotannin da ke shigo mana yanzu haka sun bayyana mana cewa wani Matashi ya auri Mata guda biyu a Jihar Adamawa. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 26 ga watan Fabrariru na shekarar 2022. Majiyarmu ta tabbatar da cewa tuni dai an daura auren, Kuma sun tare a gidansa ga baki dayansu. Cikakken rahoto na nan tafe

Sojojin Najeriya sun shirya gasar Rawa don ‘karfafa zaman lafiya’

Image
Rundunar (OPSH) a Filato ta shirya gasar raye-rayen al'adu don inganta zaman lafiya a tsakanin kabilu daban-daban a Karamar Hukumar Barkin Ladi Plateau. Ishaku Takwa, mai magana da yawun rundunar, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a cikin Jos, ya ce an gudanar da taron ne a ranar Asabar a Barkin Ladi. Da yake jawabi a wajen taron, kwamandan rundunar, Ibrahim Ali, ya ce gasar na daga cikin hanyoyi wajen samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Mista Ali ya ce sojoji za su ci gaba da daukar dabaru daban-daban wajen tabbatar da zaman lafiya don tabbatar da kwanciyar hankali ya dawo a dukkan sassan Filato. “Bari in yi amfani da wannan damar don sanya Al’ummar Filato su yi amfani da al’adunsu masu dimbin yawa wajen inganta hadin kai da zaman lafiya a tsakanin kabilu daban-daban na jihar. Babu wata mafita da ta wuce zaman lafiya kuma kyawun zaman lafiya shine lokacin da mutane suka taru don yin bikin tare ba nuna bambancin al'adunsu," in ji shi. Mista Ali ya bukaci jama’a da ...

Jaruma Hafsat Idris ta auri ɗan Janar Abacha a asirce

Image
Rahotannin sirri sun tabbatar da cewa jarumar Kannywood, Hafsat Ahmad Idris, ta yi aure a asirce jiya Asabar, 26 ga Fabrairu, 2022. Wata majiya ta kurkusa da jarumar, wadda ake wa laƙabi da Ɓarauniya saboda fim da ta yi mai wannan sunan, ta shaida wa mujallar Fim cewa an ɗaura auren ne da ɗaya daga cikin ‘ya’yan tsohon shugaban ƙasa, marigayi Janar Sani Abacha. Majiyar ta ce, “Ɗan Abacha wanda aka haifa a Fadar Shugaban Ƙasa” ne ta aura. Mujallar Fim ba ta gano wanbe ne daga cikin ‘ya’yan Abachan ba – wato tsakanin Abdullahi da ƙanen sa Mustapha. An ɗaura auren a asirce a Kano, irin yadda wasu ‘yan fim ɗin Hausa su ke yi. Hakan ya sa ba mu gano inda aka ɗaura auren ba da sadakin da aka biya da kuma waliyyan ango da amarya. Majiyar mu ta ce an tsara cewa babu wata walimar auren da za a yi kuma amarya za ta tare ne ba tare da ɓata lokaci ba.

An ɗaura auren Aisha Tsamiya jiya juma'a, duk da ta wallafa cewa an canza rana

Image
Duk da iƙirarin da ta yi jiya na cewar ba za a ɗaura mata aure a yau ba, sai ga shi an ɗaura auren fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (Tsamiya). Mujallar Fim ta ambato Aisha a jiya ta na faɗin cewa sai a watan Maris ne za a ɗaura auren nata, ba kamar yadda aka nuna a katin gayyata ba. Sai dai jim kaɗan da wallafa labarin da mu ka yi a jiya, wata majiya ta kurkusa da Aishar ta shaida wa mujallar Fim cewa tabbas za a ɗaura auren a yau Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 kamar yadda aka tsara da farko. Majiyar ta ce Aisha ta yi waccan magana ne kawai don ta basar da mutane. Lallai kuwa hakan ne ya faru, domin kuwa a safiyar yau aka ɗaura auren A’isha Muhammad Ali da angon ta Alhaji Buba Abubakar. Sai dai akasin yadda aka nuna a katin, an ɗaura auren a Masallacin Malam Aminu Ibrahim Daurawa da ke Kano, wato an canza lokaci da wurin ɗaurin auren da aka saka a kati.

Kwanan nan zamu ɗauki ƴan Batch D a shirin N-POWER - Gwamnatin Tarayya

Image
Rahotannin sun nuna cewa ma'aikatar Agaji ta Tarayya, da kare daiftila'i, da ci gaban Jama'a ta Najeriya sanar da fara shirin Npower 2022 masu cin gajiyar rukunin D.  Gwamnatin Tarayya tana gab da kaddamar da shirin N-POWER Batch D, na shekarar 2022, Wanda zai kasance za a cike Form din a Online, fom ɗin da aikace-aikacen zai kasance kyauta, Wannan yana nufin cewa duk matakan daukar ma'aikata ba za su buƙaci biyan kowane nau'i ba. Abubuwan Bukatun Rijistar N-power Batch D Takardun da ake buƙata don rajistar za su haɗa da ingantaccen ID da BVN. Dalilin lambar satifiket ɗin bankin shine don tabbatar da cewa waɗanda suka ci gajiyar shirin ba su shiga cikin rajistar rukunin D na npower na kan layi ba.

Ku Daure Ku Zabe Ni A Matsayin Shugaban Nijeriya, Lafiya Ta Kalau, Inji Tinubu

Image
Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce yana da koshin lafiyar da zai shugabanci Najeriya a zaben shekara ta 2023 mai zuwa. Ya bayyana hakan ne a Oshogbo, babban birnin Jihar Osun, lokacin da ya ziyarci Fadar Ataoja na Oshogbo ranar Juma’a. Ya ce, “Ba aikin birkilanci nake nema ba. Aikin da nake nema kwakwalwa yake bukata. Lafiyata kalau. Kawai aiki aka yi min a kokon gwiwa, kuma na warke. “Ba tseren doki zan yi ba ballantana a ce kafata ba za ta iya ba. Ina da gudunmawar da zan bayar don ciyar da Najeriya gaba,” inji Tinubu. Tun da farko dai sai da Tinubu, wanda ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya ziyarci fadar Ooni na Ife da ke Ile-Ife da kuma fadar Owa Obokun Adimula na Ijesa da ke garin Ilesa a Jihar. Tinubu ya kara da cewa, “Na zo nan ne neman tabarraki da addu’o’inku. Kun riga kun san aniyata, kun san me nake nema. Yanzu abin da nake nema a wajenku kawai shi ne hadin kai da addu’a. “Na jima ina mara wa mutane baya a nan da can, mun zaga...

'Da Zai Maka Ubansa A Kotu Bisa Kin Biyansa Kudin Kwangila Da Ya Aiwatar

Image
Babban dan Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, wato Abdulazeez Ganduje, ya yi barazanar kai mahaifinsa kotu in har ba’a biya shi cikon kudin da yake bi na kwangila ba.  A ranar 7 ga Mayu 2021 ne dai Ganduje ya bawa kamfanin Abdulazeez mai suna Global Firm Limited kwangila ta naira miliyan 189 kuma aka biya shi naira miliyan 82 bayan ya fara aikin. Amma sai dai gwamnan daga bisani ya ki biyansa cikon kudin duk da ya gama aikin. Wata majiya ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA cewa rashin biyan nasa cikon kudin na da alaka da kai karar mahaifiyarsa Hajiya Hafsat Ganduje da ya yi ga hukumar EFCC a shekarar da ta gabata. A zantawar da jaridar DAILY NIGERIAN ta yi da Abdulazeez, ya tabbatar da cewa ya yi duk iya kokarin da zai yi kudinsa su fito amma sun ki fitowa.  Ya kuma shaidawa wakilinmu cewa rashin biyan nasa na da alaka da takardar da ya kai EFCC, kana kuma da turjiya da ya yi wajen kin bada na-goro ga Gidauniyar Ganduje (Ganduje Foundation). A takardar da ya rubu...

Sabbin Hotunan Jaruma Rahama Sadau sun tayar da kura a kafar sadarwa

Image
Fitacciyar Jarumar Kannywood, Rahama sadau ta saki wasu zafafan hotuna a shafinta na sada zamunta na Manhajar Instagram. Sai dai hotunan sun tayar da kura a kafar sadarwa, inda mutane ke ta tofa albarkacin bakinsu, wasu na jindadi, wasu kuma na yi Mata Nasiha da fatan shiriya a gareta. Jarumar dai ‘yar wasa ce a masana’antar Kannywood, da Kuma Indiyan Film, wadda ta dade tauraronta na haskawa a fadin Duniya. Wace Shawara zaku bata?

Hoton Mace Musulma ta farko da ta rike mukamin janar na ‘yan Sanda a kasar Somaliya

Image
Shafin Aljazeera na Manhajar Facebook ya wallafa hotunan wata jajritacciyar Mace, Musulma ta farko da ta rike Mukamin Janar na Hukumar Jami’an tsaron ‘Yan Sanda na Kasar. Zakia Hussen Ahmed kenan, Mace kuma Musulma ta farko da ta kai mukamin Janar a Rundunar ’Yan Sandan kasar Somaliya. Wannan ya sanya mutane na ta jinjina a gareta bisa jajircewarta, akan wannan aiki nata har takai wannan mukami Wane fata zaku yi Mata? 📷: Aljazeera/Twitter

Baya ta haihu: Ba gobe zanyi aure ba, CewarJaruma Aisha Tsamiya

Image
Fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (Tsamiya) ta bayyana cewa ba a gobe Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 ba ne za a ɗaura mata aure kamar yadda aka yaɗa a soshiyal midiya. Wannan sabuwar sanarwar ta biyo bayan yaɗa wani katin gayyatar aure ne wanda aka yaɗa a soshiyal midiya, ana cewa na auren jarumar ne. A katin, an nuna cewa fitacciyar jarumar za ta yi aure a ranar Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022. A katin, wanda mujallar Fim ta gani, an bayyana sunan sahibin nata, wato Alhaji Buba Abubakar, kuma aka ce za a ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:00 na rana a masallacin Sheikh Zarban da ke Kwanar ‘Yanwanki, kusa da gidan Tanko Yakasai da ke unguwar ‘Yankaba, a Kano. Tun da labarin auren ya ɓulla a soshiyal midiya abokan sana’ar A’isha su ka shiga yi mata fatan alheri, inda kusan dukkan su sun ɗora hoton ta tare da katin auren. To amma ɗazu ɗazun ban Aisha Tsamiya ta hau Instagram ta rubuta cewa, “Assalamu alaikum, jama’a barkan mu da warhaka. Na gode da addu’o’in ku da fatan alkhairi, na ji daɗi sosai, a...

Osinbajo ya bude rukunin gidajen likitoci 78 da shaguna 78, tare da Makarantu a Borno

Image
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya je Maiduguri ne a ranar Alhamis din da ta gabata, domin kaddamar da cibiyar gwamnatin tarayya na kananan sana’o’i karo na 30, inda ya kaddamar da ayyuka hudu cikin sama da 500 da gwamnan jihar Borno, Farfesa Zulum ya aiwatar.  Mataimakin Shugaban ya isa Maiduguri ne da misalin karfe 11 na safe, inda Gwamna Zulum ya tarbe shi tare da Sanata Kashim Shettima da ‘yan majalisar tarayya da na jiha da sauran manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar. Ya iso cikin tawagar Ministoci Jiha  mai kula da masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Ambasada Maryam Katagun, Karamin Ministan Noma, Baba Shehuri wanda ya fito daga Borno, da kuma wasu ‘yan majalisar dokokin kasar daga Borno. Mataimakin shugaban kasa ya tsoko ne daga filin jirgin domin kaddamar da wani sabon rukunin gidajen likitocin da aka gina a kan titin filin jirgin a Maiduguri. Wuraren da aka tsara da kyau sun ƙunshi  78 na gidaje masu dakuna uku daga shinge 13 na gine-g...

Matsalar Tsaro: Wazirin Katsina ya Ajiye Sarautarsa

Image
Wazirin Katsina na biyar a gidan Sarautar Sullubawa, Alhaji Sani Abubakar Lugga, ya ajiye rawaninsa a yau Alhamis 24/2/2022, kamar yadda jaridun Katsina City News suka tabbatar. Matsalar ajiye sarautar tasa, ta biyo bayan wani jawabi da Wazirin ya gabatar a Ilorin Jihar Kwara a kan matsalar tsaro da kasar nan ke ciki baki daya. A taron, wajen tambaya da amsa a kan halin tsaro da Katsina ke ciki, Alhaji Sani Lugga, ya ba da bayanin kusan duk abin da manyan Katsina kan furta. Wannan jawabin nasa, wanda wasu jaridun kasar nan suka dauka a ranar Litinin 21/2/2022, ya harzuka masarautar Katsina, inda ta rubuta masa takardar tuhuma don neman ba da bayani a kan wa ya ce ya je ya yi maganar matsalar tsaron Katsina a Ilori? A bayanin nasa da ya rubuta, Alhaji Sani Lugga ya ba da hujjojinsa na cewa akwai matsalar tsaro a Katsina har ta shafi Kananan Hukumomi takwas da hujjarsa ta cewa an rufe makarantu, wasu Hakimai na gudun hijira. A ranar Alhamis Wazirin na Katsina ya ba da amsa cikakkiya mai ...

Wata Mota tayi hatsari a hanyar Lokoja, duka Fasinjoji sun rasu

Image
 Rahotannin da ke shigo mana yanzu sun nuna cewa wata Mota kirar Homa ta yi hatsari a babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja, inda duka Fasinjojin da ke motar suka rasu. Lamarin ya faru ne a ranar Talatar da ta gabata 22 ga watan Fabrariru na 2022. Majiyarmu ta tabbatar da cewa direban motar ya dauko Fasinjoji ne daga garin Benin da ke jihar Edo, zuwa jihar Kano. Sai dai a hanyar tafiyar ne wannan Lamari ya faru dasu. Allah ya jikansu da rahama.

DA DUMI-DUMI: Abubakar Maishadda Zai Angwance Aishatulhumaira

Image
Rahotannin da ke ahigo mana sun nuna cewa mai shirya Fina-Finan Hausa na Kannywood, Abubakar Maishadda Zai Angwance Aishatulhumaira Fitaccen tauraron me shirya fina-finan Hausa, Abubakar Maishadda ya saka hotunan kamin bikin shi da tauraruwar fina-finan Hausa, Aisha Ahmad Idris wadda aka fi sani da Aishatulhumaira a shafinsa. Mai shadda ya bayyana cewa yana sonta Kuma zai aureta nan bada jimawa ba 

Sarauniyar kyau ta kashe N1.6m don ta inganta kyanta, amma fuskatar ta komaɗe bata iya murmushi

Image
  Rahotanni  sun nuna cewa Likitoci sun komadar da fuskar wata sarauniyar kyau ta kasar Rasha mai suna Yulia Tarasevich,  Legit.ng  ta ruwaito. A halin yanzu Yulia Tarasevich, matashiya mai shekaru 43 bata iya rufe idanuwan ta ko murmushi bayan kashe Euro 3,000 ( miliyan N1.6) don inganta kyawunta. Hakan yasa matar mai yara biyun ta maka likitocin da suka yi mata aikin kotu, inda tayi korafi game da yadda tazo gare su da kyakyawar lafiyayyar fuska amma suka lalata. Da alamu matar mai shekaru 43, Yulia Tarasevich ba zata sake murmushi ko rufe idanuwan ta ba, har ta kare rayuwarta. An bar sarauniyar kyawun ta kasar Rasha da mokadaddar fuska bayan jerin aikin da aka mata don gyara tsufanta wanda ya ja mata kashe Euro 3,000 (miliyan N1.6), amma hakan bai sa sun yi nasara ba don haka ta maka likitocin da suka mata aikin kotun. Daily Mail ta ruwaito yadda aka wa Yulia aiki a fuska, karin mazaunai da wasu ayyuka don tsatso kyau a kwayar idanuwan ta a wani asibiti a Krasnoda...

Jarumar Kannywood Aisha Tsamiya zata yi Aure a ranar Juma'a mai zuwa

Image
Fitacciyar Jarumar a Masana’antar shirya wasan fina-finan Hausa na Kannywood Aisha Aliyu wadda aka fi sani da “Aisha Tsamiya” za ta yi aure. Labarin ya bayyana ne a wani katin ɗaurin aure da shafin “Kannywood Celebrities” ya wallafa a Facebook da kuma Instagram. Katin wanda ya fara yawo a kafafen sada zumunta ya nuna za a ɗaura auren jarumar a ranar Juma’a wato jibi kenan 25/2/2022 a Masallacin Sheikh Zarban, da ke Unguwar Ƴan Kaba Kwanan Ƴan Wanki kusa da gidan Tanko Yakasai bayan Sallar Juma’a. Katin ya bayyana sunan wanda zai auri Jarumar da Alhaji Buba Abubakar. Jarumar dai ta jima ba ta fita fitowa a sabin shirin fina-finai ko da a irin na “series” mai dogon zangon nan da ake yayi yanzu kuma bata sanar da ficewa ba daga masana’antar. Ta maida hankali kan kasuwancinta na sayar da kayan kwalliya da gyara jiki. Sai dai mun yi ƙoƙarin tuntubar Jarumar amma layinta kashe sannan mun ƙira layin wata makusanciyarta ma ita ma wayarta a kashe. Jaruma Aisha Tsamiya za ta amarce ranar Juma’a.

Dalibai a jihar Kano na fuskantar kalubalen sufuri

Image
Kamfanin daukar hoto na Blue Len's Multimedia, ya wallafa hotunan yadda dalibai maza yan makarantun boko ke samun kalubale ga harkokin sufuri yayin zuwa ko tashi daga makaranta a jihar Kano. Ya yin da aka jibge tarin motocin da gwamnatin baya da samar don daukar dalibai zuwa makaranta.  Kamfanin yayi kira ga gwamnatin Kano cewar bai kamata a cigaba da jibge tarin motocin nan a ma'aikatar ilimi ba. Ya kuma yi kira ga iyaye su tsawatarwa 'ya'yansu wajen daina kashe kudin motar da suka basu don zuwa ko dawowa daga makaranta, maimakon neman lift da suke ga masu motar Daf ko 'yar kurkura.  📷 Facebook/Abdulwahab Said Ahmad

YANZU-YANZU: Gobara ta tashi a Hedikwatar Ma'aikatar kudi ta Nijeriya dake Abuja.

Image
Gobara ta tashi a hedikwatar ma'aikatar kuɗi ta Najeriya da ke Abuja babban birnin ƙasar. Babu tabbaci kan ko me ya jawo gobarar sai dai tuni ma'aikatan kashe gobara suka isa wurin. Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun hukumar kashe gobara wato Abraham Paul inda ya ce ma'aikatansu na can suna ƙoƙarin kashe wutar. A wani saƙo da ma'aikatar kuɗi da kasafi ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce gobarar ba ta yi muni ba kamar yadda aka yi ta zuzutawa a shafukan sada zumunta inda ta ce wasu batira ne da aka keɓe suka kama da wuta a wani zaure da ke ƙasa a cikin hedikwatar ma'aikatar.

N-POWER: An fitar da waɗanda suka samu nasara a shirin Batch C2

Image
Matakai guda 4 don bincika hoton yatsa na N-Power daya dace mutum ya sane.  1) N-Power Batch C stream 2 duk mai son shiga cikin shirin dole ne ya ziyarci https://nasims.gov.ng/login 2) shiga tashar NASIMS/N-Power portal tare da imel ɗin da kuka yi amfani da su don rajistar N-Power ko ID ɗin aikace-aikacen N-Power ɗin ku. 3) Da zarar mai neman N-Power Batch C ya shiga N-Power/NASIMS portal, danna maballin "verification" da ke ƙarƙashin bayanin martabar N-Power ɗin ku don ganin matsayin ku na N-Power, sai ku ga sakon taya murna. , tare da hoton rajistar sawun yatsa. Idan kun ga wani shafi mara komai don Allah karku damu kanku ku cigaba da gwadawa ku sane akwai matsalolin hanyar sadarwa. 4) Masu neman N-Power Batch C yakamata su kunna fasalin shafin "kama hoton yatsa", da fatan za a lura idan wayar ku ba ta da kayan aikin yatsa da software don Allah ziyarci gidan yanar gizo mafi kusa don kunnawa da kammala rajistar biometric na yatsa.

DA DUMI DUMI: Sojojin Najeriya Sun Aika Da Mayaka ISWAP 10 Lahira A Borno

Image
Yadda Dakarun sojojin Najeriya suka  farmaki sansanin "Yan ISWAP a dajin tunbuktu dake Jihar Borno. Bayan kai farmaki da sojojin Najeriya suka yi, sojojin sun kone sansanin "Yantawayen da makamin gurneti.  Daga bisani, Wakilinmu ya tabbatar mana cewa, Tsagerun ISWAP 10 ne suka kone kurmus a dalilin wannan farmakin kwantar bauna da dakarun sojojin Najeriya suka kaddamar kan mayakan. Hakan ya kara bude wani fai-faine, ganin wasu "ya"yan kungiyar suka arce kana suka bar kayan yakinsu nan zube, bindigu, tare da tankokin yaki, motocin sufuri. "Wani irin fata za kuyi kan sojojin Najeriya a fagen fama ?

YANZU-YANZU: Kwankwaso ya kafa sabuwar Jam'iyya mai suna TNC

Image
A yanzu haka ana kaddamar da sabuwar Jam'iyyar ta siyasa 'The National Movement (TNM) a hukumance a Abuja.   TNM wadda tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ne ya gabatar da ita a hukumance ana gabatar da ita ga al'umma a wani taron da ake gudanarwa yanzu haka a babban birnin kasar nan.

YANZU-YANZU: Kwankwaso zai fice daga PDP

Image
Kwankwaso zai fice daga PDP, watakila ya koma ADC - Babu Maganar komawar sa APC  A kwanakin baya Jaridar Daily True Hausa ta buga labarin cewa kwankwaso da wasu jiga-jigan siyasa daga jam'iyyu daban-daban da kungiyoyi zasu kaddamar da sabuwar jam'iyya Wadanda ake sa ran zasu kafa wannan sabuwar tafiya sun hada da:  1. Prof Pat Utomi 2. Dr Usman Bugaje 3. Engr Musa Rabiu Kwakwanso, 4. Farfesa Kingsley Moghalu, 5. Sanata Saidu Dansadau, (Shugaban, NRM) 7. Hadjia Najatu Mohammed, 8. Prof Remi Sonaiya, 9.Pastor Ituah Ighodalo, 10. Prof Osita Ogbu; 11. Dr Sadiq Gombe; 12. Comrade Promise Adewusi; 13. Chief Akin Braithwaite; 14. Arc Ezekiel Nya Etok; 15. Lady Khadija Okunnu-Lamidi; 16. Comrade Olawale Okunniyi dss.  Yan siyasan sun yanke wannan shawara ne a taron samar da sabuwar jam'iyyar da zatayi fito-na-fito na jam'iyyun PDP da APC ranar Lahadi a Legas.  Jam'iyyu da kungiyoyin da suka hallara sun hada da Rescue Nigeria Project, RNP; Nigeria Intervention Movement, ÑIM;...

Rahama Sadau ta sadaukar da kudin sabon Film dinta ga Mabukata

Image
Fitacciyar Jarumar Fina-Finan Hausa na Kannywood, da Nollywood, Wato Rahama Sadau Ta Sadaukar Da Kudin Sabon Fim Dinta Da Ake Haskawa A Kano Mai Suna Nadeeya Ga Marasa Galihu. Jarumar da sadaukar da waɗannan kudade ne domin taimakawa marasa shi, don samun abinda zasu ci da sutura. Shirin film din mai dogon zango da ake harkasawa a Silima da ke jihar Kano. Zuwa yanzu dai Shirin ya fara yin nisa, Wanda tuni ta sadaukar da kudin aikin nata Wannan ya jawo mutane na ta tofa albarkacin bakinsu, sun mata fatan alkhairi da sanya mata albarka, dafatan shiryuwa. Jaridar Rariya ta ruwaito, sannan ta wallafa hotunan mutanen da aka bawa tallafin.

‘Yan Sanda sun kama wani Mutum da ya yaga Qur’ani Mai Girma a jihar Kano

Image
Wani matashin jami’in tsaro da har yanzu ba a san sunansa ba, a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda a Kano bisa zarginsa da yaga da taka wasu sassa na Alkur’ani mai girma. Wanda ake zargin mai kimanin shekaru 20 a duniya, an ce jami’an hukumar Hisbah sun ceto shi daga hannun al’ummarsa a unguwar Kuntau da ke cikin birnin Kano. Daga nan kuma aka mika shi ga ‘yan sanda kuma a halin yanzu yana tsare tare da gudanar da bincike a hannun Yan sanda. Wani dan uwa mai gidan da wanda ake zargin ke aiki mai suna Sunusi Ashiru ya shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa matashin ya tsira da ransa. Ya ce: “Ban nan lokacin da ya yi hakan amma na dawo na ga mutane da makamai iri-iri suna kokarin kashe shi. “Lokacin da na tambaye shi, sai suka bayyana abin da ya yi kuma a lokacin ne jami’an Hisbah suka kubutar da shi, daga bisani suka mika shi ga ‘yan sanda.” Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna K...

Yanzu-Yanzu: Kasa ta rufta da mutane dayawa masu hakar zinari a Nijar

Image
Rahotannin da ke shigo mana yanzu haka sun tabbatar mana da cewa kasa ta rufta da mutane masu hakar Zinare marasa adadi a jihar Maradi da ke Jamhoriyar Nijar. Yanzu haka da ranar nan ana can ana aikin tono gawarwakin mutanen da kasa ta rufta da su a jihar Maradi ta Nijar da ke aikin hakar Zinare. Kawo yanzu mun samu labari cewa akwai 'yan Najeriya su 6 daga karamar hukumar Gudu ta jihar Sokoto a cikin wadanda lamarin ya rutsa da su. Wannan dai shine karo na biyu da kasa take ruftawa da masu aikin hakar zinare a jihar ta Maradi. Ko a kwanan baya sama da mutun 100 ne su ka rasa rayukkan su a wajen wannan aiki

Jirgin Sojojin Najeriya ya yi barin wuta ga kananun yara, ya kashe 7 bisa kuskure

Image
Rahotannin da ke shigo mana yanzu sun nuna cewa Jirgin Sojojin Najeriya sun kashe kananan yara 7 a Jamhuriyar Nijar a kokarinsu na kashe ‘yan ta’adda. Jirgin saman yakin sojojin ne ya yi barin wuta akan iyakar Najeriya da Nijar amma maimakon kashe ‘yan ta’addar, sai ya kare da kashe yaran wanda ‘yan Nijar dinne. Lamarin ya faru a kauyen Nachade ranar Juma’a, 18 ga watan Fabrairu.  Gwamnan Maradi wanda kauyen ke karkashin ikonsa, Chaibou Aboubacar ya tabbatar da faruwar lamarin. Gwamnan yace yara 12 ne lamarin ya taba inda 7 suka mutu yayin da sauran ke karbarwar kukalawa a hannun Likitoci.   Gwamnan yace yayi imanin jirgin na neman ‘yan Bindiga ne yayin da ya kuskure. Saidai zuwa yanzu hukumomin Najeriya basu ce komai ba kan lamarin

Kalli bidiyon yadda ‘yan bindiga suka kone wani kauye a jihar Kebbi

Image
Bayan Kashe Al'umma Da 'Yan Bindiga Suka Yi A Yankin Shanga Dake Jihar Kebbi, Sun Sake Dawo Sun Bankawa Wani Kauye Wuta Bayan cikin jimami da radadin zafin rashin da da al'umma ke ciki na rashin rayuwar 'yan uwansu da 'yan bindiga suka kashe tare da garkuwa dawani, sun kara garzayowa wani kauye mai suna Tungar Zarumai suka bankawa garin wuta a jiya Asabar. Dukiyar al'umma da kuma abincinsu duk sun salwanta, yayinda al'ummar kauyen kowa ya tsere domin tsira da rayuwarsu. Har yanzu dai cikin zancen al'umma wannan yankin suna cikin fargaba a wannan karamar hukumar mulki ta Shanga. Wanda ake duban cewa matukar ba jami'an tsaro suka kawo dauki ba to tabbas  zasu Kara aikata wani mummunar ta'adin.

Nan ba da jimawa ba zamu rabawa talakawan Najeriya Naira Biliyan 10 - Ministan Jinkai

Image
Gwamnatin Najeriya, ta bayyana cewa nan nan bada jimawa ba zata sake bayar da tallafi ga Talakawan Najeriya. Gwamnatin ta bayyana haka ne ta bakin Ministar kula da ibtila’i da jinkai, Sadiya Umar Farouk, Inda ta bayyana cewa kudin tradermoni dubu 10 da aka rabawa ‘yan Najeriya shekaru 3 da suka gabata basu samu karbosu ba. Sai dai Sadiyar tace nan gaba za’a fara rabon kudin zango na 2 ga ‘yan Najeriya.  A wannan zagaye na 2 ana tsammanin mutane akalla 1,142,783 ne zasu amfana da lamarin injita. Cikakken rahoto na nan tafe

Duk wanda ya tafi yajin aikin ASSU, to a bakin aikinsa - El-rufai ga Malaman Jami’a

Image
  GwammaG jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufai ya bayyana masu aniyar tafiya yajin aikin ASSU cewa duk wanda ya tafi yajin aikin, to a bakin aikinsa. Wannan ya biyo bayan kokarin da Ƙungiyar Jami’o’i ASSU tace zata tafi yajin aikin Gargadin ga Gwamnatin Najeriya, bisa bijirewa umarninsu da tayi na kin cika masu sharuddan da suka gindaya masu. Gwamna El-rufai ya ce “Duk wanda yabi sahun Kungiyar ASUU a yajin aiki a bakin aikinsa” Gargadin Gwamna Elrufai ga Lakcarorin Jami'ar jihar Kaduna, KASU.

DA DUMINSA: Sojojin Najeriya sun Hallaka kwamandan ‘yan ƙungiyar ISWAP a jihar Borno

Image
Rahotannin da ke shigo mana sun nuna cewa jami’an tsaron Sojojin Najeriya, sun yi nasarar kashe miyagun ‘yan ƙungiyar ISWAP da dama sun Kuma kashe babban kwamandansu a jihar Borno. Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 13 ga watan Fabrariru na Shekarar 2022, a wani harin kwantan bauna da suka Kai masu.  An samu tabbacin cewa sojojin Najeriya sun kai farmakin  a jirgin A-29 Super Tucano a ranar 13 ga Fabrairu, 2022, sun kashe babban kwamandan ISWAP, Malam Buba Danfulani da wasu mayaka da dama a gefen tafkin Chadi a karamar hukumar Kukawa da ke jihar Borno. 

DA DUMI-DUMI: Gwamna Zulum ya baiwa matasa 152 tallafin Naira Miliya 100

Image
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bawa matasa 152 tallafin Naira N100m. Matasan da suka yi watsi da harkar daba a wata Ƙungiya. Wannan na zuwa ne biyo bayan kammala shirya musu na tsawon wata guda na horo na tsanaki kan harkokin kasuwanci. Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Juma’a ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga wasu matasa 152 da suka yi gyare-gyare wadanda suka kasance fitattun ‘ya’yan wata kungiyar ‘yan daba ta siyasa mai suna ‘ECOMOG’ a Maiduguri. Zulum ya basu wannan kudi ne domin su ja jari, su samu kasuwanci da zasu rika ciyar da iyalansu, Don samu ingantacciyar rayuwa

Yaro ɗan shekara 19 ya yiwa Malamarsa mai shekaru 28 ciki A Kasar Ghana

Image
Rahotannin sun nuna cewa an binciko wani karamin Yaro Dan kimanin shekaru 19 da yaa yiwa Malamarsa Mai kimanin Shekaru 28 Ciki A Kasar Ghana. Mahaifin yaron ne ya fito ya yada wannan labarin a shafinsa na Facebook, takanas kuma ALFIJIR HAUSA ta bibiya alamarin. Inda yake neman shawaran mutanen kan yadda Malamar daya dauko ta rika karantar da 'ya'yansa biyu tagwaye mace dana miji, ta ribaci namijin inji shi ya mata ciki. Kalamar wannan lamarin yana Yawon faruwa a sassan Duniya nan, Wanda Abu ne Wanda mutane da Allah Wai dashi.

Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun Kai hari a Karamar Hukumar Dandume jihar Katsina

Image
Rahotannin da ke shigo mana yanzu haka sun nuna cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, suna cen suna harbin mutane a garin Abasawa da ke karamar hukumar Dandume jihar Katsina. Lamarin na faruwa ne yanzu haka cikin daren nan, inda dayawan mutane suna guduwa domin ceton rayukansu. Wani mazaunin garin ya bayyanawa jaridar arewa cewa yanzu haka sun kashe mutum 1, sun kuma raunata da dama daga cikinsu. Zuwa yanzu dai ba a san adadin mutanen da aka harba ba, duk da dai wasu an dauke su zuwa babbar Asibiti don yi masu magani.

Gwamnatin Tarayyar ta bullo da sabon shirin taimakawa matasa Najeriya

Image
Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin ma'aikatar jinkai ta kasa, ta fito da wani sabon shiri da za ta taimaki al'ummar Najeriya na tsawon shekaru biyar (5). Wannan shiri zai karkata ne domin taimakawa matasa Najeriya domin dogaro da Kai. Ministan jinkai Hajiya Sa’adiya Umar Farouq ce ta bayyana haka ga Manema Labaran a ranar Laraba da ta gabata. Ta bayyana cewa nan gaba kadan zasu bayyana hanyoyin da mutane zasu domin samun wannan tallafi cikin sauki. Ku ci gaba da kasancewa da wannan shafi domin samun Cikakken rahoto.

Ahmed Musa ya baiwa tsohon ɗan wasan Super Eagles tallafin Miliyan biyu

Image
Kaftin ɗin Tawogar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa, Super Eagles, Ahmed Musa ya baiwa tsohon ɗan wasan ƙasar, Kingsley Obiekwu tallafin Naira Miliyan 2. A lokutan bayan ne dai Obiekwu, wanda da shi Nijeriya ta lashe gasar'Olympic' ta 'Atalanta 96', ya baiyana cewa ya na fama da matsin rayuwa, inda motar shi kwaya ɗaya tak ya ke haya da ita domin ya kula da iyalinsa. Tsohon ɗan wasan, wanda ya buga a Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Rangers International da ke Enugu da Udoji United, ya ce ya shiga harkar hayar mita ne sabo da matsin rayuwa. Hakan ne ya sanya Ahmed Musa ya tausaya masa, inda ya bashi tallafin Naira Miliyan 2. Ƴan Nijeriya da dama ne su ka riƙa godewa da yaba wa Ahmed Musa ta kafafen sadarwa.

Wani Matashi yasha fiya-fiya ya mutu, saboda mahaifinsa yaki yi Masa aure a jihar Katsina

Image
  Rahotannin da ke shigo mana daga jihar Katsina, sun bayyana mana cewa wani Matashi ya sha guba (fiya-fiya) ya mutu sakamakon Mahaifinsa yaki yi Masa aure. Lamarin ya faru ne a garin Kafur da ke jihar Katsina Arewacin Najeriya. Matashin mai suna Abdullahi Tasi’u ya rasu ne bayan ya hada kalanzir da Fetur tare da Gubar Fiya-fiya, inda ya rufe daki ya shanye. ‘Yan uwansa sun jiyo kukansa, Suke je domin Kai dauki, saidai a lokacin da suka shiga sun iske ya galabaita, an daukesa zuwa Asibitin Karamar Hukumar Malumfashi, sai dai kafin akai rai ya yi halinsa. Kafin ya rasu yana matukar son budurwarsa wadda yaso ace ya aureta, sai dai Mahaifinsa ya hana saboda wasu dalilai da ba a sansu ba

An kama wani mutum da matar abokinsa suna tafka lalata a marabar Jos Kaduna

Image
  Dubu ya cima, An kama wani magidanci da matar aure a maraban jos Kaduna cikin daki guda suna lalata.  Bisani an kama shine lokacin da ya tura matanshi su biyu gidan iyayensu da nufin suje sugai she da iyayen nasu a gida da daddare.  Dawowarsu ba wuya,  suka tarar da matar aure a dakin daya daga cikin matan nashi a tube tsirara, shima mijin nasu haka suntur. A cigana da bayanin dai, anan dai sukai ma kwartuwan matan duka,  suka yayyaga mata kayan da tazo dashi, kana suka barta tsirara anan  dai makofta suka tai maka mata da kayan sawa don ta sakaye jikinta.  Bayan da aka duna fuskae matar, aka gano cewa, Ashe matar abokin shi  kwarton na tane. Alokacin da Wakilin Jaridar ALFIJIR HAUSA Malam Muhammad Inuwa Zariya, ya zanta da daya daga cikin matan nashi ta shai da Masa cewa, a lokacin da mijin nasu yace su shirya su tafi su je gaishe da iyayen nasu sunyi mamaki matuka sabo da basu tan bayeshi ba yace su tafi Kuma baya barinsu fita anguwa gaba daya...

Mafi karancin albashin da ma’aikata zasu karba shi ne dubu 30 - Gwamnan Kogi

Image
 Gwamnatin jihar Kogi ta amince da aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 30,000 ga ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi. Gwamnatin jihar ta amince da aiwatar da sabon tsarin albashi ga ma’aikatan jihar nan take, tare da gyara wani bangare na tsarin. Sakatariyar gwamnatin jihar Folashade Arike Ayoade ce ta bayyana hakan bayan wata tattaunawa mai zurfi da shugabannin kungiyar kwadago a Lokoja. Ta ce jinkirin da aka samu wajen aiwatar da shi ya samo asali ne sakamakon gazawar kwamitin da aka dorawa alhakin kula da shirin na yin taro akai-akai sakamakon annobar COVID-19 da ta mamaye duniya. Madam Ayoade ta yabawa kungiyar kwadago bisa fahimta da hakurin da ta yi a duk lokacin da aka dauka kafin aiwatar da sabon tsarin mafi karancin albashin. A halin da ake ciki, shugabar ma’aikatan jihar, Hannah Odiyo, ta ce tare da sanya hannu kan yarjejeniyar sabon mafi karancin albashi na kasa, kwamitin ya kammala aikinsa cikin kwanciyar hankali ba tare da yajin aikin ba. Hakazalika, shugaban...

Zamu yi amfani da karfi wajen hana zanga-zanga - Rundunar ‘yan sanda Osun

Image
  Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta sha alwashin yin amfani da duk wata hanya da ta dace wajen dakile duk wata zanga-zanga ta kowace hanya, musamman a lokacin zaben gwamnan jihar dake tafe. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Wale Olokode ya ce rundunar ta samu labarin cewa wasu gungun mutane na shirin gudanar da zanga-zanga a jihar. Da yake gargadin mutane ko gungun mutanen da ke shirin irin wannan a jihar, kwamishinan ‘yan sandan a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Yemisi Opalola, ya fitar, ya yi kira ga iyaye da su gargadi ‘ya’yansu da su guji shiga cikin munanan ayyuka a lokacin zabe. Yayin da yake ba da tabbacin tsaro a lokacin zabukan Olokode ya sha alwashin cewa hukumomin tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tunkarar duk wani ko wasu mutane da ke yunkurin haifar da matsala tare da kawo cikas ga gudanuwarzabukan cikin tsanaki tare da tabbatar da doka.

Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya zata sake daukar sabbin ma’akata guda dubu 20

Image
Hukumar Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa za ta sake daukar sabbin ma’aikata a wannan shekara ta 2022. Shugaban Hukumar IGP Usman Alkali ya bayyana wa DW Hausa cewa akalla zasu sake daukar sabbin ma’akata guda dubu ashirin 20. Wannan ya biyo bayan karancin jami’an tsaro da ake samu a sassan kasar nan, inda za a Kara su domin bada tsaro ga al’umma Kasa. Sai dai IGP ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za su sanar da matasa hanyoyin da zasu bi wajen samun aiki a wannan hukuma ta jami’an tsaron ‘yan sanda. Cikakken Rahoto na Nan tafe...

Za mu yi kasuwanci amma muna bukatar jari – Martanin Matasan Najeriya ga Pantami

Image
Ministan da yai kaurin suna wajen kuka, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sha suka a kafafen yada labarai biyo bayan kalamansa na shawartar matasan Najeriya da su mayarda hankali kan kasuwanci maimakon neman aikin gwamnati. Yusuf Saidu Maza ya ce, "Ya kai Minista, ina so daga cikin albashinka na wannan wata ka saka mini jari saboda matsalata ce, Allah Ya saka maka da alheri." "Mungode da wanga shawara. Dan Allah Mallam wane kasuwanci kai Nima naje nariqemai wuta? ". Inji Muhammad Abubakar Abdullahi "Wane kokari kukayi na rage hauhawar kayan masarufi kasuwanci ma ya karye komai haraji haraji ribar kurarriya ce gamu masu karamin jari". Inji Ibraheem Kabyr "To Dr. Amman banji kayi magana akan jarin da matasan zasuyi Sana'arba wannan da suna samun hakan wallahi wani ko anbashi aikin Gwamnatin bazaya karɓaba". Inji Shehu Tanimu Lomolo  "Allah yabawa kowa hanya da zai rufawa kansa asiri,idan ta fannin kasuwanci ne kokuma ta fannin aikin gwamnati,...

Wani Matashi ya yiwa Shugaba Buhari fatan yin Hatsarin jirgin sama

Image
KAICO: Wani Bawan Allah Ya Yi Wa Buhari Fatan Hadari A Hanyarsa Ta Dawowa Gida Nijeriya Daga Kasar Belgium Wani Matashi mai suna Ahmed Abubakar Sadiq ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari fatan yin hadarin jirgin sama a hanyar sa ta dawo daga kasar Belgium a taron kasashen AU. Matashin ya bayyana haka ne a Shafinsa na sada zamunta na manhaMan Twitter a ranar Laraba 16 ga watan Fabrariru na 2022. Sai dai dayawan ‘yan kasar Najeriya sun yi Allah wadai da wannan fata na wannan Matashi. Abinda mutane ke tbaya shi ne Shin to shi wannan miye zai samu idan Buhari ya yi hadari ya mutu ne? Allah ka dawo da shi lafiya.

Matashi ya cinye waya kirar iPhone 11 tare da dubu 20 bayan sun yi gasa akan wasan PSG

Image
Wasu matasa gudana biyu sun sanya gasa akan wasan da aka buga tsakanin Kungiyar Kwallon kafa ta PSG da Kuma Kungiyar Real Madrid, Wanda aka yi a ranar Talata. Matashin mai suna Musa Ramos ya cinye waya kirar IPhone II bayan da tawagar wasan kwallon kafa ta PSG ta ci Madrid daya mai ban haushi a kakar wasan kofin Zakarun Turai ta 2022. Wannan ya faru ne biyo bayan kulla yarjejeniyarsa da Kaleepha AK 2Pac kan idan PSG ta yi nasara akan Madrid din zai bayar da wayar tasa ga Musa tare da kudi Naira 20,000. Rahotanni sun nuna cewa shi kuma Musa zai bayar da zunzurutun kudi har Naira dubu dari idan aka samu akasin haka. Me zaku ce?

Matashi ya sha guba sakamakon budurwarsa ta yaudareshi a jihar Kano

Image
  Rahotannin da ke shigo mana daga jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, sun bayyana mana cewa wani matashi mai suna Tijjani Abubakar ɗan asalin unguwar Gama PRP da ke yankin karamar hukumar Nassarawa, ya yi yinkurin kashe kan sa sakamakon cin amanar sa da budurwarsa tayi masa a makon nan. Lamarin ya faru ne da yammacin yau Talata 15 ga watan Fabrariru na Shekarar 2022 kamar yadda Gidan Rediyon Aminci ya ruwaito. Wakilin mu Ibrahim Aminu Rimin Kebe ya rawaito matashin ɗan kasuwa sayar da wayar hannu ta Farm Centre yayi wannan yunƙurin ne bayan budurwar da ya shirya angoncewa da ita tace a kai kasuwa, domin ta samu wanda ya fishi iya tattali da soyayya, baya ga maƙudan kudade da yake kashe mata. Gidan Rediyon ya bayyana cewa za a iya samuj cikyakkyan labarin ta cikin shirin idon mikiya da misalin ƙarfe 10 na dare.

Ku maida hankali akan kwarewa fiye da satifiket, Fantami ya gargadi matasa

Image
  Ministan harkokin sadarwa na kasa Nigeria, Sheik Isa Ali Fantami, ya gargadi matasan Nigeria, kan cewa su zama gwanaye ta fannonin kwarewa daban-daban, fiye da takardar shaida, wanda matukar suka kasance haka, to matsalolin Nigeria zasu zama tarihi da yardar Allah.  Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa, Ministan ya faɗi haka ne a wurin taron miƙa kyauta ga waɗanda suka samu nasara a gasar National Talent Hunt Challenge a jihar Katsina. Hakan na zuwa kwana guda da kungiyar malaman jami'oi ta kasa ASUU tace shaidar matakin zama shehin malamin boko (Farfesa) da wata jami'a ta baiwa ministan ba daidai bane, saboda bai cancanta ba a cewarsu, kuma zasu hukunta jami'ar da ta bashi. 

FG Ramps Up Disbursement of CBN’s N140bn Solar Intervention Fund

Image
The federal government is ramping up the disbursement of the N140 billion solar intervention fund, a facility by the Central Bank of Nigeria (CBN) to close the huge energy gap, especially in Nigeria’s rural communities. In the last quarter of 2020, the CBN had introduced the fund that would offer obligors access to a credit facility that would not exceed a maximum of N500 million, with the aim of providing affordable mini-grid solutions to rural dwelmini-grid. The apex bank posited that the pathways to energy access, financial inclusion and poverty reduction were closely linked and required rapid scale of pay-as-you-go off-grid technologies that would create a $2 billion annual market opportunity. To support the economic recovery in response to the COVID-19 pandemic, the CBN said the federal government launched the initiative as part of the Economic Sustainability Plan (ESP) to achieve the rollout of 5 million new solar-based connections. According to the CBN, the solar connection sche...

Labari Mai Daɗi: Zaku Iya Cike Rancen Covid-19 TCF Loan 2022, Shafin A Buɗe Yake

Image
FG ta dauki nauyin lamunin Nirsal TCF & AGSMEIS Covid-19 Masu sha'awar Najeriya da ba su samu damar cin gajiyar lamunin NIRsal TCF & AGSMEIS Covid-19 da Gwamnatin Tarayya ta yi ba an sake ba su damar neman lamunin NMFB NIB. Hukumar gudanarwar bankin Nirsal Microfinance NMFB ta ba da sabon sabuntawa game da lamunin Bankin Non Riba NIB. Ko da yake masu neman nasara da suka yi rajista a baya sun fara karbar takardar neman izinin zama a fadin tarayya. Bankin Nirsal Microfinance NMFB ya ba da sabon sabuntawa game da lamunin Bankin Non Riba NIB. A cewar NMFB, Sabbin Amincewar NIB sun fita. Yadda ake Neman lamunin NMFB TCF & AGSMEIS Covid-19 Tun da farko dai hukumar NMFB ta sanar da masu neman NIB cewa kada su sanya hannu a takardar karbar kadarorin kadarorin ko kaya ko wata dillali har sai sun tabbatar da cewa kayan da suka nema tun farko sun yi daidai da abin da ake kawowa. Yadda Zuku Cike: Domin Cike Wannan Damar Kuyi Amfani Da Wannan Wannan Link Da Ke A Kasa https://nibloa...